Yajin Aikin ASUU: Wata Daliba Ta Ruga Kotu

  • Ibrahim Garba

Babbar Mashigar Jami'ar Bayero ta Kano

Wata dalibar jami'a ta maka masu ruwa da tsaki a yajin aikin da Kungiyar Malam Jami'o'in Nijeriya (ASUU) ke yi a kotu.
Yajin aikin da kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa ke yi ta dau wani sabon salo, ta yadda wata daliba ta kai wasu manya kotu saboda illar cigaba da yajin aikin.
Wadanda dalibar ta kai kara sun hada da Attoni-Janar kuma Ministan Shari’ar Nijeriya da Minitan Ilimi da Hukumar Kula da Jami’o’in Nijeriya (NUC) da Majalisar Kula da Jami’ar Bayero da kuma ‘yan Kwamitin da su ka cimma yarjajjeniya da Kungiyar Malaman Jami’o’I a madadin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.

Wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya ce dalibar, ‘yar Jami’ar Bayero Kano dake aji biyar a bangaren nazarin aikin injiniya, fannin gine-gine, mai suna Zainab Garba Ahmed, tare da mahaifinta Alhaji Garba Ahmed sun garzaya kotun shari’un da suka shafi rikicin ma’aikata ta najeriya inda sukayi kara suna kalubalantar yajin aikin malaman jami’o’in da suka shafe fiye da wata biyu suna yi.


Your browser doesn’t support HTML5

COURT/ASUU


Baban na ta ya ce ya kasa ma ta aure don ta sami ilimi gashi kuma abin na neman ya faskara saboda yajin aikin malaman. Haka zalika, lauyan Zainab da mahaifinta mai suna Barrister Umar Usman Fari ya ce suna son kotun ta duba ta gani ko shin wannan yarjajjeniyar ta dace kuma ana iya aiwatar da ita? Idan kuwa kotun ta yadda cewa ‘yarjajjeniyar ba ta dace ba ko kuma ba za a iya aiwatar da ita ba, to ta kuma hama malaman cigaba da yajin aiki ba tare da bata lokaci ba.