Yakubu Gowon Yace babu Ruwan Musulunci Da Ta'addanci

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon, tare da tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter.

Janar Gowon yace bai kamata wani ya zargi Musulmi ko Musulunci a dalilin ayyukan wasu mutanen da suka kawo rashin zaman lafiya a arewacin Najeriya.
Tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon, yace ba daidai ba ne wani ya zargi Musulmi ko Musulunci da laifin wadanda suka kawo fitina da tashin hankali a yankin arewacin Najeriya ba.

Janar Gowon ya ce, "Musulmin da ni na sani, masu son zaman lafiya ne, amma irin wadannan mutane da suka zo da wani nufi ko Musulunci ba irin wanda muka sani, kuma wanda ya taimaka wajen rike kasar nan a zaman kasa daya ba, mu ba mu san wadannan ba."

Janar vYakubu Gowon yace bai kamata a kyale wadannan mutane masu tayar da fitina su bata ma Musulmin Najeriya su na da kuma martabarsu ba.

Wakilin Sashen Hausa, Nasiru Adamu el-Hikaya, ya aiko da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Janar Yakubu Gowon - Musulunci Ba Ta'addanci Ba Ne - 1:01