Yakubu Ibrahim, Matashi Mai Gyaran Kwan Lantarki a Miduguri, Borno

Yakubu Ibrahim mai gyaran kwan lantarki a Maiduguri da kayan aikinsa

Wakilin Muryar Amurka ya gamu da Yakubu Ibrahim, matashi dan shekara 18 da haihuwa wanda ya fara gyaran kwan lantarki tun yana dan shekaru tara a duniya da yanzu aka sani da suna Abba Mai Gyaran Gulob

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, ya tarar da Abba inda yake gyaran kwan lantarki a cikin Birnin Maiduguri tare da wasu kwayakwai da dama yana aiki a kansu. Matashin yana bude kwan ne ya gyara, ko ya sake wayarsu ko kuma shi farin kan

Cikin tattaunawar da suka yi, matashin yace a Kano ya koyi aikin gyaran kwan lantarki.

Idan an kai masa gyara, maimakon a zubar da kwan kamar yadda ake yi, ya kan bude kwan ya sake masa waya idan itace ta kone ko kuma ya sake masa kwalbar.

Yakubu ya fara da gyaran tocilan ne kafin ya kai ga gyaran kwan lantarki.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Yakubu Ibrahim Mai Gyaran Kwan Lantarki a Miduguri, Borno - 5' 41"