'Yan Adawa a Nijer Sun Fara Sukar Shirin Canza Jaddawalin Zabukan Kasar

A jamhuriyar Niger wani sabon cece kuce ya kunno  kai a tsakanin bangarorin siyasa bayan da wasu bayanai da aka wallafa a shafukan sada zumunta suka bayyana alamun aiwatar da gyaran fuska akan tsarin jaddawalin zabukan shekarar 2020 da 2021.

Tsarin jaddawalin da hukumar ta CENI ta bayar a taron manema labaran da ta kira a watan Nuwambar shekarar 2018 ya yi nuni da cewa a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2020 za a gudanar da zaben kananan hukumomi yayinda za a yi zagayen farko na zaben shugaban kasa hade da na ’yan majalisa a ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2020, sannan a kada kuri’ar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a ranar 21 ga watan Fabarairun shekarar 2021.

To sai dai wasu bayanan dake yawo a shafukan sada zumunta na nuni da cewa an sami canjin jaddawalin saboda haka zaben kananan hukumomi zai gudana a ranar 12 ga watan Janairun shekara mai zuwa sannan zaben shugaban kasa zagaye na farko a ranar 27 ga watan Disambar badi yayinda na ‘yan majalisa zai gudana a ranar 16 ga watan Janairun 2021, lamarin da tuni ya fara shan suka daga ‘yan adawa.

Dan majalisar dokokin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Moden Lumana Hon Soumana Sanda na cewa akwai lauje cikin nadi, yace ba cikin sulhu aka yi kundin zabenba.

‘Yan jaridar cikin gida da na kafafen kasa da kasa sun shafe sama da awa daya a ofishin hukumar zabe domin jin matsayinta akan wannan batu, sai dai aka sanar da su cewa su jira shugaban hukumar zai kira taron manema labarai ranar 22 ga watan nan na Janairu, sai dai sakatare mai kula da harkokin zabe a jam’iyyar PNDS mai mulki Boubakar Sabo yayi masu bayani.

‘Yan adawa dake kallon hukumar ta CENI a matsayin haramtacciya sun lashi takobin murkushe dukkan wani yunkurin murda harkokin zabe injisu.

Wannan kace-nacen akan maganar zabe na faruwa ne a wani lokacin da hukumar CENI ta shayo gangarar ayyukan rijistar sunayen mutanen dake bukatar takardar haihuwa da makamanciyarta a matsayin wani matakin share fagen hada kundin rajista irin na zamani Fichier Biometrique, yayinda wasu ‘yan Nijer ke ganin zai yi wuya a kammala wannan aiki kafin ranar soma zabe.

Ga karin bayani cikin sauti dag Sulei Mumuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Adawa a Nijer Sun Fara Sukar Shirin Canza Jaddawalin Zabukan Kasar - 3'25"