Wasu 'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 17 a Burkina Faso

Wasu suna kulawa da wani da ya jikkata daga harin na Ouagadougou a wani hoton bidiyo da aka dauka

Wasu da ba a san ko su waye ba, sun kai hari a wajen wani cin abinci a babban birnin Burkina Faso inda mutane kusan 20 suka rasa rayukansu yayin da wasu kuma suka jikkata.

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani wurin cin abinci a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, su ka kashe mutane 17 tare kuma da raunata wasu takwas.

Ministan Sadarwa Remi Dandjinou, ya fadi yau Litini cewa harin, wanda aka kai wurin cin abinci na Aziz Istanbul da ke Ouagadougou, an kai shi ne da daren jiya Lahadi.

Nan take dai babu wanda ya dau alhakin kai harin.

A watan Janairun 2016, wani harin da aka kai kan wani otal din alatu da kuma wani wurin shan shayi da ke kusa a babban birnin kasar ya yi sanadin mutuwar mutane 30.

Kungiyar Al-Qaida shiyyar Maghreb ta yi ikirarin kai harin a wannan lokacin.