‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Kasar Jamus

  • Ibrahim Garba

Wasu jami'an tsaron Nijar na aikin tabbatar da tsaro

Yanayin tsaro ya sake fadawa cikin rashin sanin tabbas a yankin Tilabery na Janhuriyar Nijar, bayan da wasu 'yan bindiga su ka sace wani bature dan asalin kasar Jamus.

A wani al’amari da ka iya tayar da hankalin ‘yan ayyukan agaji, musamman ma baki, wasu ‘yan bindiga sun sace wani dan kasar Jamus mai aikin agaji mai suna Joerg Lange a yankin Tilabery da ke makwabtaka da kasar Mali.

‘Yan bindigar, wadanda ake kyautata zaton sun ketaro ne daga kasar Mali bisa babura hudu, sun sace Mista Lange, wanda ke aiki da wata kungiyar agaji ta kasar Jamus mai aikin taimaka wa ‘yan gudun hijirar Mali, sun tafka wannan aika-aikar ce a wani kauye mai suna Rugar Cimanan mai nisan kilomita 30 daga garin Ayoro a yankin Tilabery a cewar Shugaban Karamar Hukumar ta Ayoro Jando Rishi.

Hukumomi sun ce Baturen ya yi amfani ne da wata motar da ya dauka haya a birnin Yamai, watakila saboda ya bad da sawu saboda bai gaya ma kungiyar a hukumance cewa zai ziyarci wannan yankin ba, bayan kuwa kauyen na Ayoru na daya daga cikin wuraren da aka bayyana cewa ya na cike da hadari.

Ga dai wakilinmu Sule Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Kasar Jamus