'Yan sandan kasar Uganda sun shiga farautar wasu 'yan bindigan da su ka sace wata ba-Amurkiya 'yar yawon bude ido tare da direbanta
WASHINGTON D.C. —
Kasar Uganda ta ce jami’an tsaronta na neman wata ba-Amurka ‘yar yawon bude ido da direbanta dan kasar ta Uganda, wadanda aka sace su shekaran jiya Talata, a wani gandun shakatawa na kasa, inda aka nuna su da bindiga.
‘Yansandan na Uganda, sun bayyana ba-Amurkar da aka sace din da Kimberly Sue Endecott ‘yar shekaru 35, da direbanta Jean Paul.
Su ka ce wasu ‘yan bindiga ne hudu da ba a san ko su waye, ba su ka sace Paul da Endecott daura da wani sansanin da ke cikin wani dajin da ke cikin gandun shakatawa na Queen Elizabeth National Park, da yammacin shekaran jiya Talata.