'Yan Boko Haram Sun Kai Harin Da Ya Hallaka Mutane 30

  • Haruna Dauda Biu

Mutanen kauyen Auno sun nuna rashin jin dadinsu lokacin da gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara kauyen bayan harin da ake kyautata zato 'yan Boko Haram ne suka kai shi a daren jiya, inda suka hallaka kusan mutane 30, suka kuma kona motoci a kauyen.

Wannan harin ya faru ne bayan da jami'an tsaro suka toshe wa maharan wata hanya, su kuma suka afka cikin jama'a suka bude wuta akan su, da motocin fasinjoji, bayan haka suka kona motoci 18, da kayayyaki.

Wasu da suka shaida lamarin, sun ce sun ji harbe-harbe sai kuma suka ga ana ta kona mutane da motoci.

Jama'ar sun kuma nuna damuwarsu game da rashin jami'an tsaro a wurin, da zasu ba su kariya.

A saurari rahoto cikin sauti daga jihar Bornon Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Boko Haram Sun Kai Harin Da Ya Hallaka Mutane 30