'Yan Democrat Na Kara wa a Nevada

Election 2020 Changing Nevada

Masu zabe sun fara kada kuri'a a jihar Nevada da ke yammcin Amurka, don zaben dan takarar da zai kara da Shugaba Donald Trump a watan Nuwamba.

Wannan zabe na daya daga cikin muhimman zabukan sharar fage da za su kai ga zaben fidda gwani da za a yi nan gaba a cikin wannan shekara.

Shi ne kuma karo na uku da ‘yan takarar na Democrat ke kara wa a neman tikitin jam'iyyar.

A bayan an yi wasu zabukan a jihohin Iowa da New Hampshire.

Sai dai ba kamar Iowa da New Hampshire ba, wadanda ke da gagarumin rinjayen al'umar fararen fata, Nevada, jiha ce da ke da gaurayen al’umomi.

Rabin al'umarta fararen fata ne, kashi 30 Hispaniyawa, kashi 10 Amurkawa ‘yan asalin Afirka, sannan kashi 10 kuma 'yan asalin yankin Asiya.

Bisa al'adar siyasar Amurka, sai 'yan takarar da suka fi samun karbuwa sun kara a wasu zabukan sharar fage kafin a kai ga zaben fidda gwani, inda za a fitar da dan takarar jam'iyya da mataimakinsa.