'Yan Gudun Hijira daga Tafawa Balewa Na Bukatar Komawa Asalinsu Bayan Shekaru 25

Gwamnan Bauchi Barrister M.A. Abubakar

Al'ummomin Tafawa Balewa a jihar Bauchi dake gudun hijra sun bukaci a taimaka masu su kowa asalinsu bayan sun kashe shekaru ishirin da biyar suna gudun hijira biyo bayan rikicin da yankinsu ya fada ciki a wancan lokacin.

Domin tabbatar da bukatarsu, alummomin sun mika kokensu ne ga shugaban riko na karamar hukumarsu Alhaji Aminu Umar Danbaba, wazirin Tafawa Balewa.

Alhaji Ibrahim Musa daya daga cikin shugabannin al'ummomin yace sanin kowa ne cewa wadanda ba Siyawa musulmi ba basa zaune cikin garin Tafawa Balewa. Yace sun rubuta wasika zuwa gwamnan jihar har da shugaban kasa akan bukatarsu.

Suna rokon gwamnatocin jiha da na tarayya da su taimaka mutanensu su samu su koma asalinsu. Akwai wadanda aka haifa cikin shekaru ishirin da biyar da watanni bakwai da suka gabata da basu san inda suka fito ba. Lokaci yayi da yakamata 'ya'yansu su san asalinsu. Alhaji Musa yace bai kamata a ce dan kasa ya kuntata a kasarsa ko menene kabilarsa ko jinsinsa ko addininsa.

Alhaji Suleiman Muhammad Danbauchi shi ma yace mutanen Tafawa Balewa sun koka sun ce sun gaji da gudun hijira. Suna son su koma gidajensu. Duk inda suke yanzu ba'a komi dasu domin har yanzu suna gudun hijira ne.

Shugaban karamar hukumar Tafawa Balewa na rikon kwarya Aminu Umar Danbaba ya bayyana takaicinsa dangane da halin da al'ummomin suka samu kansu a ciki kana yace ya fara tuntubar sauran kabilun dake yankin kan batun.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Gudun Hijira daga Tafawa Balewa Na Bukatar Komawa Asalinsu Bayan Shekaru 25 - 2' 44"