'Yan Jam'iyyar Democrat Sun Kuduri Aniyar Kada Trump A Zaben 2020

‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Democrat a Amurka sun gwabza muhawara a daren jiya Laraba a wani babban taron kemfe na zaben shekarar 2020 dake tafe da aka yi, dukan su muradin su shine su kada shugaba Donald Trump na jam’iyyar Republican bayan wa’adi daya a fadar White House.

Wadda aka fi maida hankali akai ita ce Sanata Elizabeth Warren, daga jihar Massachusetts dake arewa maso gabashin Amurka wadda ra’ayoyin ‘yan kasar suka nuna tana kusa-da-kusa da tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden daga jam’iyyar Democrat, masu farin jinin jama’a da zasu fafata da shugaba Trump a zaben da za a yi ranar 3 ga watan Nuwamba na shekarar 2020.

Ms. Warren ta fadawa jama’ar da suka taru a Miami dake jihar Florida, da kuma miliyoyin jama’ar da suka kalli muhawarar a talabijin, cewa tana so ta maida gwamnati hannun jama’a.