'Yan kasuwa A Kano Sun Koka Kan Sabon Tsarin Amfani Da kudi.

Ginin kasuwar sayar da hannayen jari a Legas.

Tsohon kakakin kungiyar masu hada hadar kudin canji, Dr. Adamu Danjuma Isa, yace sabon tsarin amfani da kudade da dan kasuwa ya ajiye Banki yana da kyau, amma ga 'yan kasuwa tsarin illace a garesu.

Dr. Adamu Isa yace idan ka saka kudin cikin ajiyar kamfani, sannan ka nemi fidda su banki zai dauki kashi biya biyar, idan kuma a ajiyarka ka saka kudaden, ka nemi daukan kudaden sai banki ya caji kashi uku.

Dr. Adamu ya bada misali da wani kamfani mai suna Infranza da aka nemin su rika hulda da shi gameda ajiyar kudi, anan ma ya nuna matsaloli da suke fuskanta.

'Yan kasuwa da suke cinikin tufafi a kasuwar kantin kwari sun koka da wannan tsari. Malam Sa'idu Malaman 'Yaya, yace a hukumance sai tayu wannan tsari ne mai kyau amma a gun 'yan kasuwa wannan ba karamar matsala ne ba. Ya bada misalin cewa idan dan kasuwa ya ajiye Naira milyan daya idan yayi niyyar daukansu, banki zai caje shi Naira dubu 30. Yace wannan lamari yana janyo musu cikas.

Daya daga cikin 'yan kasuwan, yayi kira da babban Bankin ya sake yiwa shirin garambawul, kuma a bullo da shi sannu a hankali cikin shekaru uku maimakon bullo da kashi lokaci guda.

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Bankin Najeriya