'Yan Majalisa Sun Kara Biliyan N23.7 A Kasafin Kudi Don Aljihunsu

Bukola Saraki A Wata Tattaunawa Da VOA Hausa

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa Sanata Danjuma Goje, ya ba da hujojjin yin kari a kasafin kudin bana, inda yayi bayani cewa an ware wa Hukumar kula da Yankin Arewa Maso Gabas karin Naira biliyan 45.

Jihar Zamfara an ware mata Naira Biliyan 10, sannan an ware wa 'yan Majalisa da suka bar Majalisar wani kaso har naira biliyan 23. da digo 6, a ciki har da Shuguban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce sun yi kare-karen ne domin al'umma, inda ya kara da cewa zai kawo wata doka da za ta sa a kafa Hukumar Arewa Maso Yamma, saboda a tallafa wa jihohin Zamfara, Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Kebbi da Sakkwato domin a taimaka wajen yaye wa wadanda iftila'i ya auka wa na rashin tsaro.

Sanata Gaya ya ce wannan kasafin zai kara dankon zumunci tsakanin Majalisa da bangaren zartaswa da ma Shugaba Mohammadu Buhari.

Wani abu da ya dauke hankali a kasafin na bana shi ne, Majalisar ba ta sauya kudin gangar danyen man fetur ba daga dalar Amurka $60 da Shugaba Buhari ya mika wa Majalisar.

Medina Dauda daga Abuja Najeriya ta aiko muna da wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Majalisa Sun Kara Biliyan N23.7 A Kasafin Kudi Don Aljihun Su 2'30"