Jiya Lahadi wasu fitattun 'yan Majalisar Dattawan Amurka sun yi kira ga fadar Shugaban Amurka ta White House da ta fito fili ta fayyace matsayin zaman mayakan Amurka a Janhuriyar Nijar bayankashe sojojin Amurka hudu da aka yi, a wani kwantan bauna da aka masu a farkon wannan watan.
A wasu hirarrakin da aka yi da su a lokuta dabam dabam a shirin gidan talabijin na NBC mai suna, "Meet the Press," Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican da kuma Shugaban 'yan Democrat marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sen. Charles Schumer sun ce su na goyon bayan yunkurin da Sanata John McCain ya yi a makon jiya na neman cikakken bayani game da wannan harin da kuma matsayin Amurka a yaki da ISIS a wannan kasa ta Yammacin Afirka. Da Graham da Schumer sun ce ba su san akwai sojojin AMurka da dama a Nijar ba.
Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis ya gaya ma Graham da McCain, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Soji a makon jiya cewa rundunar sojin Amurka na dada karkata yakin da ta ke yi da ta'addanci zuwa Afirka.
Jami'an Amurka na ganin wata kungiyar ta'adda a yankin, wadda kuma ta ke da alaka da ISIS, ita ce ta kai harin na Nijar. To amma har yanzu hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon na binciken yadda al'amarin ya faru.