'Yan Majalisar Kamaru Na Muhawarar Kasafin Kudi

Paul Biya, Shugaban Kasar Kamaru.

‘Yan majalisar dattawa a Jamhuriyar Kamaru na ci gaba da zaman tattaunawa game da gyaran lamarin kasafin kudaden da za a kashe a kasar a shekarar 2016.

Sun kwashe kwanaki goma suna ta faman tattauna yadda ya kamata a ce an aiwatar da hada-hadar kashe kudaden shekarar da za a shiga.

Har ma da maganar yadda za a inganta yadda kasar zata samu kudaden shiga daga cikin gida da kasashen ketare.

A karshe tattaunawar na son cimma matsaya da zata samarwa kasar ci gaba a bangarori daban-daban musamman kayan masarufi.

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Muhaman Auwal garba ya aiko mana da wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Majalisar Kamaru Na Muhawarar Kasafin Kudi - 1'33''