‘Yan Majalisun Dokokin Najeriya Sun Shirya Yiwa Kasar Addu’a Ranar Alhamis Mai Zuwa Domin Samun Zaman Lafiya

Ginin majalisun tarayyar Najeriya

A karon farko, abubuwan dake faruwa a Najeriya sun sa ‘yan majalisun dokoki na tarayya shirya taron yiwa kasar addu’a ranar Alhamis mai zuwa]

Yanzu a kalla kowane mako sai an ji barkewar wata tarzoma ko gtashin hankalin da wasu lokutta ke hadawa da asaran rayukka a Najeriya. Dalili ke nan da ‘yan majalisun dokoki na tarayyar kasar suka kudurta kiran taron addu’a domin a samu zaman lafiya.

Ranar Alhamis mai zuwa za’a gudanar da taron addu’ar da ake kyautata zaton shugaban kasa da mataimakinsa da ma wasu manyan gwamnati na yanzu da na da zasu halarta.

A cewar ‘yan majalisun, yin addu’ar zai sa a samo mafita daga abubuwan da suka addabi kasar, a kuma kawo karshensu.

‘Yar Majalisar Dattawa, Binta Garba ta ce tura ce ta kai bango, har suka shirya daukan wannan matakin, ganin cewa babu daya cikin manyan addinai biyun da suka yi maganar masifun da ake fuskanta, amma duk sun yi maganar ci gaban al’umma.

Shi kuwa wanda ya wakilci ‘yan majalisar wakilai, Timothy Ngolu Simon, yace sun dauki matakin ne cikin gaggawa da fatan Allah zai yayyafawa matsalar ruwan sanyi. Bayan addu’ar ana kyautata zaton ‘yan majalisun zasu koma mazabunsu su jaddada bukatar zaman lafiya.

Medina Dauda na da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Majalisun Najeriya Sun Shirya Yiwa Kasar Addu’a Ranar Alhamis Mai Zuwa Domin Samun Zaman Lafiya - 2' 40"