‘Yan Najeriya Naci Gaba Da Bayyana Ra’ayin su Game Da Garanbawul A Majilisar Ministoci.

  • Ladan Ayawa

Nigeria's President Muhammadu Buhari swears in ministers into his cabinet in Abuja, Nigeria November 11, 2015. Buhari swore 36 ministers into his cabinet on Wednesday, five months after his inauguration. Buhari won March elections after vowing to crack do

'Yan Nigeria naci gaba da bayyana raayin su game da yiwa majilisar ministocin Nigeria garanbawul musammam ma ganin kalaman da daya daga cikin su tayi kwanan nan

Har yanzu ana ci gaba da cece-kuce game da Majalisar Ministocin Najeriya.

Wannan kuwa yana zuwa ne tun daga lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya koma gida daga Ingila inda ya kwashe kwanaki masu yawa yana jinya.

Da yawan ‘yan Najeriya sun zura ido kuma sun kasa kunne suji yadda zata kaya a taron ministoci mai zuwa wanda aka saba yi ranar kowace ranar Laraba.

Wannan batun neman yin garanbawul ya kara fitowa fili ne bayan kalaman da ministar mata Aisha Jummai Alhassan tayi na jaddada goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria Alhaji Atiku Abubakar

Yanzu haka dai wannan kalamin Ministan Matan yana ci gaba da haifar da raayoyi mabanbanta a cikin kasa.

Ga Ibrahim Abdsulazeez da Karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Najeriya Naci Gaba Da Bayyana Ra’ayin su Game Da Garanbawul A Majilisar Ministoci.2'49