‘Yan Nijar Sun Koka Da Harin Boso 

Sojojin Cadi da Nijar sun kashe 'yan Boko Haram, Maris 19, 2015

‘Yan kasar Jamhuriyar Nijar sun nuna kaduwa da asarar rayukan sojojin kasar kimanin 30 bayan kazamin harin da kungiyar Boko Haram ta kai a yammacin juma’ar da ta gabata a garin Boso dake yankin Diffa.

Sannan sun yi korafi akan rashin komawar shugaban kasar ta Nijer Isuhu Mahamadu gida, daga wani taron kungiyar bunkasa tattalin arzikin yankin yammacin Afrika na ECOWAS, da yake halarta a birnin Dakar a Senegal domin jajantawa mutanen da harin ya rutsa da danginsu.

Yankin Diffa da ke kan iyaka da Najeriya ya jima yana fama da hare-haren kungiyar ta Boko Haram, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama da kuma dukiyoyi.

Baya ga haka dumbin ‘yan gudun hijra daga Najeriya suma sun kwarara yankin na Diffa domin neman mafaka.

Saurari ra’ayoyin ‘yan Nijar kan wannan hari wanda ya rutsa har da wasu sojojin Najeriya biyu kamar yadda wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma ya tattaro mana:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Nijar Sun Koka Da Harin Boso – 3’06"