'Yan Raji a Sudan Sun Goyi Bayan Haramta Kaciya

Masu rajin kare hakkin mata a Sudan da hadin kan kungiyoyin da ke fafutukar kare walwalar yin addini, sun goyi bayan matakin da kasar ta dauka na haramta kaciyar mata.

A cikin makon da ya gabata ne, gwamnatin wucin gadin kasar ta sanya hannu kan wani kudurin doka wanda ya haramta yi wa mata kaciya, tare da ba da damar a ci tara da kuma kama duk wadanda aka samu da laifin na tsawon shekara uku.

A cewar Majalisar Dinkin duniya, 9 cikin mata 10 a Sudan, tsakanin ‘yan shekara 15 zuwa 49 sun fuskanci irin wannan al’ada ta kaciya, wacce za ta iya janyo matsaloli ga kwakwalwa ko ga jikinsu.