‘Yan ta’adda Na Kokarin Raba Kan ‘Yan Najeriya - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi kira ga ‘yan Najeriya, da kada su bari ‘yan ta’adda su raba kan al’umar kasar ta hanyar fakewa da addini.

Buhari ya yi wannan kira ne, kwana biyu, bayan da rahotanni suka nuna cewa, reshen kungiyar IS da ke yammcin Afirka na ISWAP, ya kashe wasu Kiristoci hade da wasu Musulmi.

“Na yi matukar bakin ciki tare da kaduwa bisa kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda mutane marasa tausayi da rashin imani suka rike su, suke kuma bata sunan addinin Islama” a cewar wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta kara da cewa, “kada mu bari a yi amfani da wata kafa, ‘yan ta’adda su gwara kanmu - ta hanyar hada Kiristoci da Musulmi fada, saboda wadannan mutane marasa imani ba wakilan addini Islama ba ne kuma ba jakadun miliyoyin Musulmi da ke sauran sassan duniya ba ne.”

A cewar Shugaba Buhari, “babu wani Musulmin kwarai, da zai rika ambatar “Allahu Akbar” yayin da yake kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, domin Al Qur’ani mai girma, ya sha yin Allah wadai da irin wannan aiki na shedanci.”