'Yan Ta'addar Daji Sun Kashe Mutane 15 a Jihar Taraba

Shirin bison wadanda 'yan ta'addar daji su ka kashe a Gassol

A cigaba da aika aikar da 'yan ta'addar daji ke yi a sassan Najeriya, wannan karon sun far ma mutanen Gassol, inda su ka hallaka a kalla 15 daga cikinsu.

Mutum akalla 15 aka kashe sakamakon harin da 'yan fashin daji suka kai a kauyen Karekuka na Jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya a wani harin da aka fara tun da tsakar ranar Juma'a aka kuma sake kai wa jiya Asabar.

Kazalika, an jikkata mutanen da ba a san adadinsu ba a harin, wadanda ke jinya kuma yanzu haka wasun su na Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke birnin Jalingo, kamar yadda kakakin 'yan sanda na Taraba ya shaida wa Muryar Amurka.

Tuni aka yi jana'izar mutanen a garin da ke cikin Karamar Hukumar Gassol, akasarinsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Sallar gawar wadanda aka kashe

'Yan sanda sun ce tun farko mutanen garin ne suka kama ɗaya daga cikin 'yan fashin bayan wani hari da suka kai kuma suka kashe shi, inda su kuma suka kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya.

Sai dai wasu rahotanni na cewa 'yan bindigar sun sake yi wa Garin Gidado kawanya da safiyar ran Asabar amma sun tarar ba mutane a garin.

Mai magana da yawun Hukumar 'Yan Sanda, SP Abdullhi Usman, ya ce an tura jami'an tsaro yankin don kwashe gawarwakin mutanen bayan harin.

Dan majalisar mai wakiltar Bali da Gossol a Majalisar Wakilain ta Taraiyyar Nigeria Honarabul Abdullasalam Gambo Mubarak ya tabbatar cewa ya sanar wa rundunar sojojin sama da na kasa kuma sun ce za su tashi dakarunsu domin ganin an tarwatsa yan bindigar.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Salisu Garba:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kashe Mutane 15.mp3