'Yan Tawaye Sun Kwace Ikon Babban Birnin Damokaradiyar Janhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Sojojin Damokaradiyar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

‘Yan tawayen jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun kwace ikon babban birnin kasar abinda ya tilasawa shugaban kasar Francois Bozize arcewa daga Bangui.

Shaidu sun bada rahoton jin karar manyan makaman fada a birnin da asubahin yau Lahadi yayinda ‘yan tawayen suke kutsawa babban birnin kasar, a kan hanyarsu zuwa kwace ikon fadar shugaban kasa.

Hukumomi basu bayyana a hukumance inda shugaba Bozize ya gudu ba. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci ta bakin wani mai ba shugaban kasa shawarwari da ya nemi a saya sunansa cewa, shugaban kasar ya ketara zuwa Damokaradiyar Jamhuriyar Kwango yau Lahadi da asuba.

Da farko ‘yan tawayen sun kutsa Bangui jiya asabar suka yi watsi da da kiran da Firai Ministan kasar ya yi da su zauna a tattauna da nufin gudun zubar da jinni.

Tun farko jiya asabar a cikin hira da sashen Farasanci na wannan tashar wani kakakin gwamnatin yace, Firai Minista Nicolas Tiangaye ya yi kira ga kungiyar ‘yan tawaye ta Seleka Alliance ta tuntubi gwamnatin hadin guiwa ta kasar domin shawo kan matsalar ta hanyar lumana. Sai dai ‘yan tawayen Seleka sun ce ba zasu tattauna ba sai shugaba Bozize ya sauka daga karagar mulki.