Yanayi Mai Kama Da "Jaura" Na Ratsawa Ta Cikin Amurka

Miliyoyin Amurkawa na fuskantar wani yanayi na matsanancin sanyi da ba su taba gani ba, yayin da wata iska mai tsananin sanyin gaske ke ratsawa ta cikin kasar.

Masu hasashen yanayi sun ce mai yiwuwa, wannan yanayi da ya fara daga daren Talata zuwa wayewar garin Laraba, ya zama tarihi a kasar.

Tuni dai har gwamnonin jihohin Illinois, Winsconsin da Michigan suka ayyana dokar ta baci a yankunansu.

A can yankin jihar Dakota ta Arewa, sanyin iskar, ya kai kasa da maki 32 na ma’aunin digrin Celcius, yayin da ya kai kasa da maki 52 a wasu yankunan jihar Minnesota.

Ya zuwa yanzu, an samu rahotanni da ke cewa wasu mutum hudu sun mutu sanadiyar wannan tsananin sanyi.

Ita dai wannan iska ta hado ne tun daga yankin tsakiyar yammcin Amurka, ta hada da gabashi, ta kuma dangana da can yankin kudanci jihar Florida.