'Yancin Bayyana Ra'ayin 'yan Jarida na da Iyaka - inji John Tsok

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada 'yanci game da bayyana ra'ayi amma kuma akwai iyakoki.

A kwanan nan ne wata jaridar kasar Faransa ta wallafa wata mujallar Allah waddai. Abinda ya janyo suka daga sassan duniya daban-daban. Hakan yasa muryar Amurka ta tuntubi manyan ‘yan jarida a Najeriya da Janhuriyara Niger game da ‘yancin jama’a da na ‘yan jarida akan bayyana ra’ayi.

Mr John Tsok, tsohon shugaban kungiyar ‘yan jaridun Njeriya reshen jihar Plato, cewa yayi, kowace kasa na da dokoki da tsare-tsaren ta.

Kundin tsarin mulkin Najeriya na aluf dari tara da cisi’in da tara, sashi na 39 sakin layi 1, ya ba jama’a da sauran ‘yan jarida damar bayyana ra’ayi. Amma kuma a wani bangaren kundin tsarin mulkin, ya bada iyaka akan damar bayyana ra’ayi, wanda suka hada da rubutun batanci ko cin zarafin wani, inji Mr. Tsok.

Shi kuma Malam Zada Bawa, shugaban gidan radiyon Dalol FM na janhuriyara Niger cewa yayi bai kamata ‘yan jarida su wallafa kowane irin labari ba. Kuma yayi Allah wadai da abinda ya faru a kasar Faransa.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yancin bayyana ra'ayin 'yan jarida na da iyaka - 4'20"