Yara da Rikicin Boko Haram Ya Shafa Suna Neman Tallafin Kayan Karatu

Yaran da rikicin Boko Haram ya daidaita dake zaune a Jos

Yaran da yanzu suke Jos jihar Filato sun fito ne daga jihohin Borno da Adamawa , jihohin da rikicin ya fi shafa a arewa maso gabashin Najeriya

Yaran da rikicin Boko Haram ya tilasta masu zuwa Jos sun bukaci masu hannu da shuni da su taimaka masu da littafai da wasu kayan karatu a sansanin da suke domin samun ilimi mai inganci.

PLATEAU: Ginin makarantar yaran

Yayinda Muryar Amurka ta ziyarci wani gidan marayu da ake kira House of Rikap ta samu yara fiye da dari biyu wadanda shekarunsu ke tsakanin ukku zuwa goma sha biyar. Yawancin yaran daga jihohin Borno da Adamawa suka fito.

House of Rikap ke kokarin ciyar da yaran da samar masu da sutura da makaranta. Makarntar da aka yi masu an yita ne da kataki da kwanukan jinka ne lamarin da ya sa ruwa da iska kan damesu.

Wasu cikin yaran sun zanta da Muryar Amurka. Wani yaro daga Borno yace ya arce ne daga Gwozah lokacin da 'yan Boko Haram suka shiga garin nasu. Da farko sun taka da kafa ne zuwa Kamaru, sai kuma Yola daga bisani suka isa Jos.

A inda suke yaron yace basu da dakunan karatu masu inganci kamar yadda aka gani a hoton makarantar dake wannan rahoton.

Shi Adamu Joshua Dabawa wanda ya fito daga jihar Borno yace sun yi wata ukku cikin tsaunukan duwatsu saboda rikicin Boko Haram din. Zuwansu Jos aka taimaka masu da makaranta su cigaba da karatunsu tare da taimakon mutanen dake basu abinci.

Shugaban wata kungiyar Greater Tomorrow dake tallafawa yaran Paul Okoku yace kodayake yana zaune ne a Amurka amma hankalinsa na tashi idan ya ji labarin abun da Boko Haram ke yi dalili ke nan yake bada taimako.

Shi ma Labaran Muhammad wanda aka fi sani Khalifa ya kira jama'a masu hannu da shuni su taimakawa yaran. Yace yaran sun zama abun tausayi, abun takaici bisa ga halin da kasar ta tsinci kanta. Bai kamata a tsaya sai gwamnati ko manyan kamfanoni sun kawo taimako ba. A tashi a taimaka masu ko ta yaya.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yara da Rikicin Boko Haram Ya Shafa Suna Neman Tallafin Kayan Karatu - 4' 01"