Yariman Masarautar Birtaniya Ya Kamu Da Coronavirus

An tabbatar da cewa, Yariman Birtaniya Charles ya kamu da cutar coronavirus.

Wata sanarwa a jiya Laraba, ta ce yariman ya nuna wasu alamun kamuwa da cutar, to amma dai yana cikin koshin lafiya.

An auna matarsa Camilla aka kuma tarar ba ta da cutar. Sai dai kuma sun killace kansu a wani gida a Scotland.

A halin da ake ciki kuma kasuwannin duniya sun cira a yau Laraba, bayan shugabannin Amurka sun bayyana daukar matakin kai daukin kudi akan annobar cutar coronavirus.

Hannayen jarin Kamfanin Nikkei na Japan ya haura da kashi 8 cikin 100, yayin da kamfanin Hong Kong, Seng ya cira da kashi 4 da kuma kamfanin Shangai Index ya haura da kaso 2 cikin 100.

Hanayen jarin kasasen Turai ma sun farfado da safiyar yau, yayin da hanayen jarin Amurka suka nuna alamun samun riba idan kasuwar ta bude zuwa can anjima.

Rashin tabbas game da kwayar cutar da irin illar da zata yiwa tattalin arziki ya rikita kasuwannin duniya na tsawon wattani, yayin da aka zabtare farashin hannayen jari lokacin da gwamnatoci da manyan bankuna suka shiga fafutukar daukar matakan ceto kasuwar ta duniya.