Yau Ce Ranar Maulidi

Shaikh Dahiru Bauchi shugaban kungiyar Tijjaniya daya daga cikin shugabannin addinin Musulunci a Najeriya

Yau ce ranar da musulmi a duk fadin duniya ke bukuwan Maulidi, ranar da aka haifi Annabi Muhammad (SAW) domin nuna murnar zagayowar ranar

Al'ummar Musulmi kan yi anfani da ranar wajen gudanar da addu'o'i da karatun al-Qur'ani da kuma yin sadaka.

Liman Shehu Rimaye jigo a darikar Tijjaniya reshen jihar Neja yayi tsokaci akan ranar. Yace an ce kafin zuwan Annabi duniya tana cike da duhu da jahilci amma sanadiyar haihuwarsa Allah ya sa duniya tayi haske. Baicin hakan Allah ya yayewa duniya kafirci da jahilci.

A wannan lokacin matasa ma suna anfani da ranar wajen gudanar da wakokin begen nuna yabo ga tsayayyen halitta.

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnatin jihar Neja ta taya al'ummar Musulmi murnar bikin Maulidi. Amma gwamnan ya gargadi wadanda suke bikin tare da rufe hanya domin yin hakan suna tauye hakkin wasu ne. Yace idan zasu yi gangamin bikin su gayawa mahukumta da zasu taimaka su bi gefen hanya ba tare da rufeta ba. Gwamnan yace babu kayau a tauyewa wasu hakkinsu saboda ana biki.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar Maulidi - 2' 54"