Jiya Ba Yau Ba: Ghana Ta Cika Shekaru 61 Da Samun 'Yancin Kai

Magajiyar Kent (Duchess of Kent) tana taka rawa tare da Kwame Nkrumah, firayim ministan Ghana na farko a wajen wata gagarumar liyafar da aka shirya a ranar 6 Maris 1957, domin murnar 'yancin kan kasar Ghana wanda ta samu a wannan rana.(AP Photo/Staff/Burroughs)

Kwame Nkrumah

Yarima Philip, magajin Edinburg, yana zaune tare da firayim ministan Ghana, Dr. Kwame Nkrumah a lokacin wata liyafar da aka shirya musamman domin zuwan Yariman birnin Accra a ranar 23 Nuwamba, 1959, domin ziyarar mako guda a Ghana. (AP Photo)

Firayim ministan Ghana, Dr. Kwame Nkrumah, da gwamna-janar na Ghana, Lord Listowel, suna tarbar Yarima Philip, Magajin Edinburg a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Accra domin fara ziyarar mako guda a kasar Ghana, 23 Nuwamba, 1959. (AP Photo)

Malaman gargajiya su na barbada maganin  nema wa shugaba Kwame Nkrumah albarka a lokacin da zai shiga cikin majalisar dokoki domin bude taro a shekarar 1965.

Dr. Kwane Nkrumah, firayim ministan Ghana, ya sauka a fadar Balmoral a matsayin bakon sarauniya Elizabeth ta Biyu. Wannan hoto da aka dauka ranar 12 Agusta 1959, ya nuna (Hagu zuwa dama) Yarima Charles; Sarauniya Elizabeth; Dr. Nkrumah; Gimbiya Anne da kuma Yarima Philip. AP Photo)

Dr. Kwane Nkrumah, firayim ministan Ghana, ya sauka a fadar Balmoral a matsayin bakon sarauniya Elizabeth ta Biyu. Wannan hoto an dauka ranar 12 Agusta 1959, AP Photo)

Mayakan gargajiya na Ghana a titunan Accra a shekarar 1960, a bayan da Dr. Nkrumah ya ayyana kauracewa Afirka ta Kudu domin nuna kyamar mulkin wariyar launin fata

Shugaban Amurka John Kennedy tare da shugaba Kwame Nkrumah na Ghana a filin jirgin saman Washington national a ranar 8 Maris, 1961.

Firimiya Nikita Khrushchev na Tarayyar Soviet ya tashi daga kan kujerarsa a babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya domin yin musafaha da shugaba Kwame Nkrumah na Ghana wanda ke komawa kan kujerarsa bayan wani jawabin da yayi ranar 23 Satumba 1960. (AP Photo)