Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Rohingya Dake Bangladesh Sunce Baza Su Koma Myanmar Ba


Wasu 'yan gudun hijirar Rohingya a kan iyakar kasar Bangladesh
Wasu 'yan gudun hijirar Rohingya a kan iyakar kasar Bangladesh

Al'ummar musulmin Rohingya dake gudun hijira a kasar Bangladesh sun ce har yanzu akwai yanayin kuntatawa a jihar Rakhine.

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya ce dakarun tsaron Myanmar na cigaba da keta hakkokin bil’adama akan sauran musulmin Rohingya da suka rage a arewa maso gabashin jihar Rakhine.

A wata rubutacciyar sanarwa da Andrew Gilmour, mataimakin babban sakataren kula da hakkokin jama’a ya fidda yau Talata, ta ce “ana cigaba da aikata ayyukan assha akan ‘yan Rohingya, yayi la’akari da ‘yan gudun hijirar da suka isa sansanonin da suka cika makil a makwabciyar kasar Bangladesh kwanan nan.

A halin da ake ciki kuma kasar Bangladesh ta mika sunayen ‘yan gudun hijira 8,000 ga Myanmar a makon da ya gabata don a fara shirin maida su kasashen su. Amma ‘yan Rohingya sun ce ba so su koma Myanmar saboda har yanzu yanayin jihar Rakhine, inda suke da zama yayi masu tsauri.

Ko Ko Linn, wani shugaban al’ummar ‘yan gudun hijirar Rohingya, ya ce ‘yan Rohingya ba zasu koma Myanmar ba saboda kawai gwamnati ta dauki matakin tilasta masu komawa wasu unguwarni nesa da kauyukan da suke da.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG