Yau ne Makon Shayar da Jarirai Nonon Uwa

A duk ranar 5 ga watan Agustan kowace shekara an ware ranar a matsayin makon shayarda nonon uwa.

A duk ranar 5 ga watan Agustan kowace shekara an ware ranar a matsayin makon shayarda nonon uwa, wanda hukumar lafiya ta duniya da asussun tallafawa kananan yara ta ware.

An ware wannan ranar ne domin bunkasawa da kuma wayar da kan iyaye mata dangane da mahimmancin nonon uwa.

Nonon uwa na daya daga cikin mahimman abinci da uwa yakamata ta ba jaririnta wanda yake kunshe da sinadaren gina jiki masamman ma a wurin taimakawa jariri domin samun koshin lafiya.

A wannan shekaran an fi maida hankali ne domin fito da alfanun shayarda nonon uwa a wunkurin kawar da fatara da talauci da ake fama da shi a fadin duniya.

Hukumar lafiya ta duniya, tace baiwa jariri nonon uwa zalla har na tsawon watani shida yana da alfanu matuka.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau ne Makon Shayar da Jarirai Nonon Uwa - 2'33"