Yaya Aikin Hajjin Wadanda Suka Bar Makwabta Cikin 'Yunwa?

Dabbobi.

A duba kasuwar dabbobi da ninka farashinsu a bana, wani dan kasuwa yana aibunta masu hali dake tafiya aikin hajji, yayinda suka bar baya da 'yunwa.

kasuwar dabbobi ta Sara dake Gwaram a jahar Jigawa, farshin dabbobi sun nunka na shekarun baya baya nan, kamar yadda Dr. Mohammed Bello na jami'ar Dutse dake jahar ya gayawa Nasiru Adamu El-Hikaya ta wiyar tarho.

Dr. Bello yace shekarun baya dabbobin suna wajajen dubu hamsin da 'yan kai, amma bana ya taya wata dabba kan Naira dubu dari da biyar, yana neman a yi ragi. Yace wasu dabbobin kudinsu ya haura Naira dubu dari da hamsin.

Malamin Jami'ar yace babu abunda ya janyo haka illa burin jama'a, domin babu magamar faduwar darajar Naira da tsawwala farashin dabbobi.

Amma wani dan kasuwa Ado Adamu, yana zargin wasu masu hali da yin watsi da hali da makwabtansu suke ciki,su kama hanya zuwa aikin hajji.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Layya ba wajibi bane idan baka da hali