Yunkurin Kawo Karshen Fadan Manoma Da Makiyaya A Najeriya

Fulani makiyaya

Rikici da kan taso tsakanin Manoma da Makiyaya a Najeriya bai tsaya a bangare daya kawai ba, kama daga Arewacin kasar zuwa Yammaci da Kudanci ana samun rikice-rikice akan Gonaki ko kuma Dabbobi.

Ministan cikin gida Abdurrahman Bello Danbazau, yayi yunkurin kawo karshen tashin hankalin da akan afku tsakanin Manoma da Makiyaya, inda ya shirya wani taro da aka hadu don zama a duba yadda za a shawo kan lamarin, wanda jami’an gwamnati sukayi. Sai dai Ministan yace akwai wani babban taro da za’ayi nan gaba wanda zai hada da duk bangarorin biyu da kuma gwamnati, domin zama a fuskanci yadda za ayi gyara, a kuma sami zaman lafiya.

Isah Tafida Mafindi, wanda yake Manomi kuma Makiyayi, yace wanann zamani ne na canji inda har Ministoci ke aikin kawo zaman lafiya tsakanin Manoma da Makiyaya.

Shima shugaban kungiyar habaka Matasa na jihohin Arewa Imurana Wada Nas, na ganin wannan yunkuri abune mai kyau, domin duk abinda za ayi ya amfani talakawa yana da kyau don sune suka zabi shugabanninsu.

Jawabin bayan taron na cewa idan ana son zaman lafiya ta dore tsakanin Manoma da Makiyaya, to sai fa an hada kai baki daya a duk lokacin da za ayi shawarwarin abinda kowa zai aikata idan zai shafi zamantakewa. Kuma a rika tuntubar manya daga dukkan fannonin biyu.

Domin karin bayani saurari rahotan Madina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Yunkurin Kawo Karshen Fadan Manoma Da Makiyaya A Najeriya - 2'50"