Yunwa Ce Ta Sa Wasu Mata Saida Kuri'unsu A Maiduguri- Inji Kakabe

A yayinda a wasu jihohin Najeriya aka fara bayyana sakamakon zabe a wasu kuma ana ci gaba da tattara alkaluman don sanarwa jama’a irin gwanayen da suka zaba su shugabance su har tsawon shekaru 4.

Alhaji Shettima Kakabe shugaban jam’iyyar PDP a birnin Maiduguri, ya zargi jam’iyyar APC da sayen kuri’ar mata.

A hirar su da wakilin muryar Amurka Haruna Dauda Biu, Kakabe ya ce yunwa ce ta addabi mata da sauran jama’a shi ya sa suka saida kuri’un su, idan ba don haka ba, da APC ba ta kai labari ba.

Shi kuma wakilin APC wajen tattara alkaluman zabe a Maiduguri, Alhaji Aliyu Usman Alkali, ya ce wannan zargin ba gaskiya ba ne kuma idan wani yana da shaida sai ya fito da ita.

Garba Usman Sadiq, shugaban hukumar tattara alkaluman zabe na birnin Maiduguri ya tabbatar da cewa akwai wuraren da aka sami kuskure wajen hada alkaluman zabe daga bangaren jami’an zaben, amma ya yayi imanin cewa ba da gangan aka yi wannan kuskuren ba kuma an riga an yi gyaran da ya kamata.

A yanzu haka dai hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta kasa a ke jira ta fidda sakamakon ta a hukumance.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Yunwa Ce Ta Sa Wasu Mata Saida Kuri'unsu A Maiduguri- Inji Kakabe - 4'11"