Za'a Bude Tashoshin Jiragen Ruwa a Arewacin Najeriya

Tashoshin jiragen ruwa shiddane zasu fara aiki a arewacin Najeriya wanda basu da ruwan teku.

Tashoshin jiragen ruwa shiddane zasu fara aiki a arewacin Najeriya wanda basu da ruwan teku, kuma samarda wa’yannan tashar yazame wajibi saboda a yanzu haka jirgin ruwa mai daukar sunduki kusan dubu biyar zuwa guda yafara zuwa tashar jirgin ruwa ta birnin Ikko, kuma ikko ne kadai irin wannan jirgi ke zuwa daga cikin kasashen Afirka ta yamma da jirgin ruwan kebi domin jigilar kaya, kafin wannan jirgin yafara zuwa Najeriya ada jirgin da yake zuwa kawo sunduki wato (container) yana daukar dubu daya da dari biyar kawai ne amma ana samun cinkoso a tashar jirgin.

Fara shigowar irin wannan jirgin yana nufin kara kudin shiga Kenan ga kasa, kuma za’a samu rashin bata lokaci a wajen fidda kaya kasancewar yana daukar sama da sa’a ashirin da hudu ada kafin mutum ya fidda kayansa daga gurin masu tsaron shiga.