Za a Fara Gwajin Allurar Rigakafin Coronavirus

Katafaren kamfanin sarrafa magunguna na Amurka, Johnson & Jonhson, ya bayyana cewa zai fara gwajin allurar rigakafin cutar Coronavirus zuwa watan Satumba.

Ya kuma ce rigakafin zai iya samuwa domin amfanin gaggawa zuwa farkon shekara mai zuwa.

Jiya Litinin, kamfanin ya ce shi da Ma’aikatar Lafiya da Harkokin Jama’a ta Amurka sun sadaukar da sama da dala biliyan guda a aikin kirkirowa da kuma gwajin rigakafin.

Ya ce idan har aka samu nasarar gwajin akan bil adama, to zai shirya samar da allurorin sama da biliyan daya.

Shugaban kamfanin Alex Gorsky ya fada wa shirin “Today” na gidan talabijin din NBC cewa alamu na nuna cewa allurar rigakafin za ta yi aikin da ake bukata.