Yayin da a baya aka ga kamar wannan karon Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo za ta yi zaben Shugaban kasa cikin lumana, sai kuma gashi alamomin baya-bayan nan na nuna cewa kasar na iya fadawa cikin dambarwar siyasa.
WASHINGTON D.C. —
Jami'ai a Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (Congo) sun ce za a jinkirta bayyana sakamakon zaben Shugaban kasa har sai wani lokaci cikin satin nan.
Hukumar zaben kasar ta na wata ganawa yau dinnan Lahadi kan batun jinkirta bayyana sakamakon zaben.
Shugaban Hukumar Zaben Kongo (CENI) Corneille Nangaa ya ce, "Ba abu mai yiwuwa ba ne a bayyana sakamakon a yau dinnan Lahadi. Mu na samun cigaba, to amma ba mu kammala komai ba tukunna."
Nangaa ya ce Hukumar zaben ta tattara kashi 47% na akwatuna daga runfunan zabe a fadin kasar, wadda ba ta da kyawawan hanyoyin sufuri.