Za'a Kaddamar Da Riga Kafin Cutar Sankarau Ga Yara Sama Da Miliyan 6 A Nijar

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar kiwon Lafiya a Jamhuriyyar Nijar zata kaddamar da shirin riga kafin Cutar Sankarau, ga yara kanana fiye da Miliyan 6, na tsawon mako daya daga gobe Talata a duk fadin kasar. Biyo bayan wani rahoto da ya tabbatar da bullar cutar a jihar Damagaram.