Za A Kai Hama Amadou Jinya A Kasar Waje

Hukumomin Nijar sun bayyana cewa rashin lafiyar madugun 'yan adawan kasar, Hama Amnadou, yayi tsananin da har shugaba Issoufou Mahamadou ya bayarda umurnin a kai shi jinya a kasar waje.

Yau talata da maraicen nan ne ministan shari'a na Nijar, kuma kakakin gwamnati, Marwa Amadou, yace jiya suka samu labarin rashin lafiyarsa ya tsananta, har aka tura likitansa yaje ya duba shi.

Amma daga bisani, kwararrun jami'an kiwon lafiya sun je domin duba shi, inda suka ce yana fama da matsananciyar gajiya, kuma akwai bukatar kulawa daga wurin kwararrun likitoci, wadanda babu su a Nijar, tilas ne sai an kai shi kasar waje.

Sai dai kuma, jami'in na gwamnatin Nijar bai fadi lokacin da za a fitar da Hama Amadou zuwa kasar wajen ba, bai ma fadi kasar da za a kai shi ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Za A Kai Hama Amadou Jinya Kasar Waje - 2'00"