Za A Mayar Da 'Yan Gudun Hijirar Angola Kasarsu

  • Ibrahim Garba

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon

Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR a takaice, ta ce ‘yan gudun hijiran Angola sama da 43,000 ne da ke zama a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo

Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR a takaice, ta ce ‘yan gudun hijiran Angola sama da 43,000 ne da ke zama a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo za a maida su gida bisa yaddarsu a wata mai zuwa.

Wannan shirin da aka sanar das hi jiya Laraba, ya nuna cewa za a fara mayar da ‘yan Angolan ne daga ran 4 ga watan Yuli a kuma kammala a farkon shekara mai zuwa.

‘Yan Angola da dama ne su ka gudu daga kasarsu bayan barkewar yakin basasa a 1975. ‘Yan Angola kimanin 80,000 ne a yanzu ke zama a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Congo ya ce gwamnatin kasar za ta cigaba da bayar da masauki ga duk wani dan Angolan day a zabi cigaba da zama a kasar.