ZABEN 2015: Daga Abuja Za'a Bada Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

Dakin tantance sakamakon zabe na daya.

Hukumar zabe ta INEC na cigaba da tara sakamakon zaben shugaban kasa wanda zata sanarda da kasar daga cibiyar da ta kafa a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

A cibiyar za'a tantance duk wani sakamako da ya fito daga kowace jiha.

Nick Dazan jami'in INEC yace da zara sun bude cibiyar da zata tantance sakamakon zaben shugaban kasa zasu gayyaci 'yan jarida su sa ido ga ayyukan da zasu yi. Masu sa ido daga kasashen ketare suma zasu kasance a wurin.

Hukumar tace kawo yanzu bata bada wani sakamako ba akan zaben shugaban kasa. Saboda haka duk wani bayyani da wasu ke yayatawa ta yanar gizo jama'a su yi fatali dasu. Yace da yawa cikin wadanda ke yayata sakamakon zaben suna da nasu ra'ayoyi kuma ba kwararrun 'yan jarida ba ne. Komi sai 'yan jarida sun tabbatar, sun tantance kafin su bazawa duniya. Amma masu yada sakamako a gidajensu suke suna yada abun da suka ga dama.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Daga Abuja Za'a Bada Sakamakon Zaben Shugaban Kasa - 2' 11"