Zaben fidda dan takarar jam'iyar PDP ya bar baya da kura a jihar Kebbi

PDP

Gwamnan jihar Kebbi alhaji Sa’idu Usman Nasamu Dakingari yace ya zabi Bello Sarkin Yaki a matsayin dan takarar gwamna domin cika alkawarin da ya yi naai kyautatawa al’ummar jihar.

Zaben fitar da gwani a jihar Kebbi ya fuskanci cece kuce da dama tare da korafe korafe da ya sa aka dakatar da shi domin neman masalah,a daga baya kuma aka bayyana sunan Bello Sarkin Yaki wani tsohon soja a matsayin dantakarar jam’iyar PDP a jihar.

A cikin hirarsu da Sashen Hausa. Gwamnan jihar alhaji Sa’idu Usman Nasamu Dakingari yace a lokacin da ya dauki rantsuwa bayan zabensa ya yi alkawarin cewa, zai kyautatawa al’ummar jihar kuma ba zai yi wani abinda zai cutar da suba.

Bisa gacewarshi, dalilin da yasa ya zabi wanda zai gaje shi , shine domin cika alkawarin da yayi cewa, bayan kamala wa’adin mulkinsa zai zabarwa jihar wanda zai gajeshi na kwarai, kuma ya hakikanta cewa Bello Sarkin Yaki shine ya dace da rike wannan mukanin domin ya taka rawar gani a aikinsa an gani.

Wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna ya aiko da cikakken rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Siyasar jihar Kebbi