ZABEN NAJERIYA: Amurka Ta Bi Kadin 'Yancin Talaka

Kungiyar Tawagar Turai Da Ta Sa Ido A Zaben Najeriya, Ta Fitar Da Rahoton Karshe

Gwamnatin Amurka ta dauki matakin tsabtace tsarin zaben Najeriya ta hanyar da zata shafi manyan ‘yan siyasa masu ikon fada a ji.

Gwamnatin Amurkan ta dauki wannan matakin ne wajen hana wadansu ‘yan siyasa takardun izinin shiga Amurka, wadanda ta bayyana cewa suna da hannu a magundin zabe da aka yi a jihohin Kogi da kuma Bayelsa a zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara,

A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin ofishin jakadancin Amurka na Najeriya, sanarwar tace,

“A cikin sanarwar da aka fitar ranar 24 ga watan Janairu, 2019, gwamnatin Amurka ta ce zata dauki matakai masu tsauri da suka hada da hana takardun bisa ga wadanda suka yi wa tsarin damokaradiya zagon kasa ko kuma haddasa tashin hankali. A watan Yuli shekara ta 2019, muka sanar da hana takardun bisa ga wadansu daidaikun jama’a wadanda suka yi zagon kasa a zabukan da aka gudanar a watan Fabrairu da kuma Maris 2019.”

Sanarwar ta kuma bayyana kara daukar irin wannan matakin kan wadanda suka yi katsalandan a zabukan da aka gudanar a jihohin Kogi da Bayelsa a watan Nuwamba 2019, da kuma wadanda suke hana ruwa gudu a zabukan da ake shirin gudanarwa a watan Satumba a jihohin Edo da kuma Ondo, wadanda gwamnatin Amurka ta ce suna cin karensu ba babbaka, ba tare da kula da yadda hakan ke shafar al’ummar kasar ba.

'Yan Daba Dauke Da Makamai Ranar Kammala Zabe a Kano

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ranar Litinin, 14 ga watan Satumba ta bayyana cewa, “an dauki wannan matakin ne kan daidaikun jama’a, kuma ba zai shafi ‘yan Najeriya ba," Sanarwar ta kara da cewa, “wannan matakin da aka dauka manuniya ce kan manufar ma’aikatar harkokin wajen Amurka na hada hannu da gwamnatin Najeriya wajen cimma burinta na shawo kan cin hanci da rashawa, da kuma karfafa damokaradiya, da yin adalci a mulki da kuma mutunta hakkin bil’adama.”

Sanarwar ta kuma yabawa ‘yan Najeriya wadanda suka bada gudummuwa a zaben shekara ta 2019 a duk fadin kasar domin karfafa tsarin damokaradiya. Ta kuma bayyana cewa, Amurka zata ci gaba da hada hannu da kasar wajen karfafa damokaradiya da mutunta hakkin bil’adama da kuma wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasashen biyu.

Amurka ta kuma kushewa duk wani tashin hankali da kuntatawa da cin hanci da rashawa da zai cutar da ‘yan Najeriya da kuma kawo cikas a zabukan da ake shirin gudanarwa a jihohin Edo da ondo, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da suka hada da hukumar zabe, da jam’iyun siyasa da jami’an tsaro su mutunta tsarin damokaradiya, su gudanar da zaben da zai zama karbabbe cikin kwanciyar hankali da lumana.