An Fara Zaben Shugaban Kasa a Misra

Mata Sun Fito Jefa Kuri'a

Ana zaben shugaban kasa a Masar, zaben da masu lura da al'amura suka ce zai ba shugaba Abdel Fatah El Sisi damar ci gaba da zama akan karagar mulki.

A yau Litinin ne al’ummar kasar Misra suka fara gudanar da zaben da ake kyautata zaton cewa zai bai wa shugaba Abdel Fatah El-Sisi damar ci gaba da mulki har na tsahon karin wasu shekaru hudu.

Abokin hamayyar Sisi mutum guda ne tal mai suna Moussa Mustafa Moussa, wanda a can baya mai cikakken goyon bayan Sisi ne kafin ya shiga siyaysar.

Kafin zaben na yau, an kame da yawa daga cikin ‘yan takarar, wasu kuma an tilasta musu su janye kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Jam’iyyun adawa sun yi kira ga mabiyansu kan su kauracewa zaben wanda za’a dauki kwanaki 2 ana yi.

Ana sa ran sakamakon zai fito ne a ranar 2 ga watan Afrilu.