Ana Kan Kirga Kuri'u a Zaben Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo

  • Ibrahim Garba

Wata mace goye da diyarta a wurin kada kuri'a

Ana kirga kuri'a a zaben kasa na Jamhuriyyar Demokaradiyyar Kongo. Bayan ga jinkirin da aka samu an kuma fuskanci rashin tsari a runfunan zabe.

Ana kan kirga kuri'u a zaben shugaban kasa na Janhuriyar Demokaradiyyar Kongo, wanda aka gudanar ranar Lahadi bayan wani jinkiri, zaben da ka iya zama karon farko da kasar za ta samu sauyin gwamnati cikin lumana, bayan kimanin shekaru 60 da samun 'yanci.

An fuskanci rashin tsari a runfunan zabe da dama, ciki har da bacewar rajistar masu zabe da kuma lalacewar na'urorin zaben wanda ya sa aka kai har dare ana gudanar da zaben, don haka ala tilas jami'an zaben su ka yi ta amfani da tocila wajen gudanar da zaben. Wata tawagar masu sa ido kan zaben, wadda Cocin Katolika ta kafa ta ce ta samu rahotannin 544 na lalacewar na'urorin zabe.

A ranar lahadi an samu Tashe tashen hankula, wanda yayi sandiyan mutuwar mutane 4 a kudu maso gabashin Kivu, ciki harda dan sanda da wani ma’aikacin zaben, wandanda aka zarga da yin magudin zabe.