Zafafan Kalamai Basune Zabe Ba, Kyautatawa Talakawa Itace Ansa

Gwamnan jihar Taraba: Darius Dickson Ishaku

An fara ca-car baki a tsakanin 'yan siyasa a Najeriya, gabanin zaben 2019.

Yayin da ake haramar gudanar da babban zabe a Najeriya, yanzu haka an soma musayar kalamai a tsakanin gwamnan jihar Taraba Arc. Darius Dickson Isiyaku, da jam’iyyun adawa kan batun ayyukan da gwamnatin PDP a jihar ke cewa ta aiwatar.

Wannan dambarwar dai na zuwa ne yayin da ake haramar soma babban zabe a Najeriya, inda gwamnan jihar Taraban Akitet Darius Dickson Isiyaku, ke zargin cewa jam’iyyun adawa a jihar na shirin amfani da bakin haure, domin kwace gwamnatin PDP a jihar, zargin da 'yan adawa ke musantawa.

Gwamnan jihar wanda ya soma da zayyano wasu nasarorin da yace gwamnatin PDP ta kawo jihar a zamaninsa.

Daga nan kuma sai gwamnan yayi zargin cewa tuni suka bankado wani yunkuri, na wasu da ya kira 'yan adawa na shigo da bakin haure zuwa jihar a lokutan zabe, batun da ya bukaci sarakuna da su sa ido.

Sai dai kuma da alamun kalaman gwamnan jihar bai yiwa 'yan jam’iyar APC dadi ba. Ambassada Hassan Jika Ardo, jakadan Najeriya a kasar Trinidad da Tobego,wanda tsohon shugaban jam’iyar APC ne a jihar, yace suna da ja ga kalaman gwamnan jihar.

Baya ga jihar Gombe, jihar Taraba itace ta biyu da babbar jam’iyar adawa ta PDP ke mulki a jihohin arewa maso gabas shida, wanda kuma lokaci ne ke iya tabbatar da yadda zata kaya, yayin da babban zabe ke kara matsowa.

Ga rahoton wakilin sashen hausa na Muryar Amurka Ibrahim Abdul’Aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Zafafan Kalamai Basune Zabe Ba, Kyautatawa Talakawa Itace Ansa 2'30"