Zaman Dalibai da Gwamnatin Hong Kong Holoko ne Hadarin Kaka

Zaman dalibai da jami'an gwamnatin Hong Kong

Zaman akan teburin shawara da daliban Hong Kong suka yi da jami'an gwamnati bai tsinana komi ba tamkar banza ma ta fishi

Dalibai dake zanga-zangar kwadayin demokradiyya a Hong Kong sun nuna bacin ransu bayan hawa teburin shawarwari da gwamnati, inda suke cewa jami’an basu saurari kukansu ba.

Shugaban daliban Hong Kong Lester Shum yace yayi matukar mamaki yadda gwamnati ke cigaba da bukatar daliban su amince da jaddawalin zabe da China ta tsara na shekarar 2017.

“Ina matukar mamaki da al-ajabi da dagewar da gwamnati tayi akan cewa sai mun amince da fasalin zaben da China ta gindaya. Gaskiya gwamnati bata nuna karfin gwiwa da gaskiya wajen warware wannan takaddamar siyasa ba.”

Wani mai zanga-zangar wanda ya bukaci a kirashi Tam, ya bayyana bacin ranshi.

“Babban sakataren gwamanti Carrie Lam tace watakila a samu damar kawo sauyi nan gaba, amma bata ce ga lokacin ba, saboda haka mu ganin wannan muke a matsayin zancen banza, zancen wofi.”

A jawabinta na bude tattaunawar, Sakatariyar Lam tayi kira ga shuwagabannin daliban da su kawo karshen zanga-zangar makonni uku da suka share suna yi, inda ta kira su masu jawo rabuwar kawuna, kuma masu jawo tsaiko a harkokin kundun tsarin mulkin Hong Kong.

Lam, wadda itace ta biyu a shugabancin Hong Kong din tace kasar bata da ‘yancin kanta, saboda haka bata da zabin yadda zata gudanar da harkokin zabenta.