Zanga zangar Kasar Nicaragua Ta Hallaka Akalla Mutane Goma

Masu zanga-zanga a Nicaragua

Zanga zangar da aka fara tun ranar Laraba domin kin amincewa da yunkurin yiwa shirin fansho garambawul ta hallaka mutane goma a Nicaragua

A Nicaragua, zanga zangar da aka fara tun ranar Laraba don nuna adawa da shirin garambawul ga kudaden fansho ko ritaya ta halaka mutane akalla 10, ciki harda wani dan jarida wanda ya ke bada rahoton abubuwan da suke faruwa kai tsaye ta dandalin Facebook. Wasu kungiyoyin rajin kare hakkin Bil'Adama suka ce yawan wadanda suka halaka ya kai 25.

A jawabinda ya yi wa al'umar kasar ta gidan talabijin ranar Asabar, shugaba Daniel Ortega, yace a shirye yake ya gudanar da shawarwari kan wannan batu domin hana "iyalai ci gaba fuskantar tashin hankali." Ortega ya kara da cewa, shugabannin 'yan kasuwa ne kadai zai gana da su.

Kammala jawabinsa ke da wuya, masu zanga zanga suka sake fitowa kan titunan biranen kasar, ciki harda babban birnin kasar Managua, bayan zaman dar dar ta sassauto ranar jumma'a.