Ziyarar Buhari Birtaniya Kwalliya Na Biyan Kudin Sabulu

Shugaba Buhari tare da Farai Ministan Ingila David Cameron

Fadar gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwa dan gane da ziyarar da shugaba Mohammadu Buhari ya kai kasar Ingila, tare da ci gaba da tarurruka da ganawa da yake da muhimman mutane na kasashe daban daban.

Da cewa wannan ziyarace da tayi nasarar gaske ganin irin muhimman matakan da shugaban ya yadawa kasashen ketare domin tabbatar da cewa an yaki cin hanci da rashawa a duk fadin duniya baki da daya.

Shugaba Buhari dai ya bayyana cewa akwai bukatar a kafa kwamitoci a kowacce kasa, na daukar matakan hana walwalar wayanda aka zarga da irin wannan sace sace, kuma ya nuna damuwarsa kan cewa Najeriya tana asara dalar Amurka Miliyan Dubu 7 akowacce shekara, a dalilin sace sace Mai da akeyi da kuma cin hanci da rashawa da akeyi cikin kasar kai tsaye.

Mallam Garba Shehu, Kakaki a fadar gwamnatin Najeriya, yace lalle wannan tafiya kwalliya ta biya fiye da kudin sabulu a wannan tafiya.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Buhari Birtaniya Kwalliya Na Biyan Kudin Sabulu - 3'52"