Zumuncin Musulmi Da Kiristan Arewacin Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Hadin kai tsakanin Kirista da Musulmi kan sa su rinka yin garkuwa ga juna a lokutan ibadar juna.

A matsayin wani bangare na bukukuwan Sallah, Musulmi da Kirista sun nuna hadin kai a kaduna
Musulmi da Kirista na cigaba da amfani da lokacin Sallah wajen kara dankon zumunci tsakaninsu. Ko a jiya ma sai da wasu fitattun Musulmi da Kirista su ka yi taro a garin Kaduna na jadda muhimmancin zumunci tsakanin Kirista da Musulmin arewacin Nijeriya, a matsayin wani bangare na bukukuwan Sallah Karama.

Wakilinmu a Kaduna Isah Lawan Ikara ya ruwaito wani kwararre a harkar ilimin zamani mai suna Mr. Mataimaki Tom Maiyashi na cewa dole ne fa mabiya su canja yadda su ke samar wa kansu shugabanni a kasar matukar ana son cigaba. Ya ce baragurbin shugabanni ke haifar da baragurbin al'umma da nau'ukan cibaya. Shi kuma Sheikh Rilwanu Gwangwan ya ce adalcin shugabanni ne kadai zai sa kasa ta cigaba ta fuskoki daban daban. Ya ce al'mundahanar shugabanni na kawo cikas iri iri.

Bishop Samuel Usman kuwa, cewa ya yi wasu mutane ne kawai ke rudin 'yan Nijeriya da banbancin addini don su rinka juya su yadda su ke so. Yayin da shi kuma Manjo Yahaya Shinko ya ce da gangan aka cusa wa 'yan arewacin Nijeriya banbancin addini don a nakkasa yankin arewa. Shugaban Kungiyar Hadin Kan Al'ummar Arewacin Nijeriya da ta shirya taron, Alhaji Adamu Aliyu kuwa ya ce makasudun taron shi ne a hada kawunan Kiristan arewacin Nijeriya da Musulmin arewacin Nijeriya don amfanin yankin.

Your browser doesn’t support HTML5

Zumuncin Musulmi Da Kiristan Arewacin Nijeriya - 2:30