Kafin ya shiga siyasa, Obi dan kasuwa ne wanda ya rike mukamai da dama a wasu masana’antu masu zaman kansu, ciki har da Next International Nigeria Ltd, da Guardian Express Bank Plc, da sauransu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga Kiristoci da sauran al’ummar kasar da su bada gudummawarsu wajen ganin an gudanar da zabe nagari badi.
Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen bukukuwan Kirsimetin bana, dillalan kifi a Inugu sun bayyana damuwarsu, kan yadda suke fuskantar karancin ciniki da suka danganta da rashin kudi a hannun jama’a.
Jama’a da dama na ci gaba da fita gudanar da harkokinsu a fadin kudu maso gabashin Najeriya duk da cewa wani bangare na kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ya tilastawa al’ummar yankin zaman gida na tsawon kwana biyar daga ranar 9 ga wannan watan Disamba.
Gwamnatin Jihar Abia da likitoci masu aiki a karkashin ta sun kasa cimma matsaya kan basukan albashin da Likitocin ke bin ta, bayan zantawar da bangarorin biyu suka yi.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ta jaddada bukatar shigo da masu nakasa cikin lamuran yau da kullum domin kawo ta su gudummawa ga ci gaban kasar.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu, ta ce an kubutar da Rev. Fada Victor Ishiwu na Cocin Katolika da wasu ‘yan bindiga suka sace a yankin Nsukka na Jihar da sanyin safiyar ranar Asabar da ta gabata.
Gwamnatin jihar Inugu tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Faransa, AFD, zata kashe kimanin dala miliyan hamsin don samar da ruwan sha a fadin birnin Inugu, babban birnin jihar.
Kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar Inugu ta yi kira da a yi sauye-sauye a bangaren kiwon lafiya na kasar don rage ko magance kaurar da likitoci ke yi zuwa kasashen waje a kokarin neman inganta rayuwarsu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatin jihar Imo sun kafa wani kwamiti na musamman, don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya da ke Inugu ya gudanar da shirin gwajin ido tare da bada magani kyauta.
An yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta saki Mazi Nnamdi Kanu madugun kungiyar IPOB, da ke fafutukar kafa kasar Biafra, bayan kotu ta wanke shi.
Daruruwan jama’a na ci gaba da ficewa daga karamar hukumar Ohaji Egbema ta Jihar Imo, inda ambaliyar ruwa ta lalata sama da gidaje 1000 da gonaki da dama a ‘yan kwanakin da suka wuce.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da gina tashar wutar lantarki mai karfin megawatt goma a kogunan Otamiri da kuma Nworie da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.
An bukaci majalisun dokokin Najeriya da su kirkiro tsarin dokar gine-gine don shawo kan matsalar rushewar gidaje da ake yawan gani a sassan kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake kai ziyara Jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar don kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ta kammala, duk da barazanar 'yan aware.
Yayin da bangarori daban daban na hukumomin Najeriya ke kintsawa don tinkarar babban zaben Najeriya na 2023, su ma 'yan sanda ba a bar su a baya ba.
Yayin da hukumomi na ci gaba da inganta dabaru wajen samar da maslaha ga matsalar tsaro da kasar ke fama da ita, ‘yan sanda dai a jihar Kros Riba da ke kudu maso kudancin Najeriya sun ce suna samun gagarumar nasara akan miyagun laifuka a fadin jihar.
Malaman jami’a a kudu maso gabashin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan zanga-zangar wuni biyu da kungiyar kwadago zata fara gudanarwa yau Talata don bai wa malaman jami’a hadin kai a yajin aikin da su ka kwashe kimanin wata shida suna yi kan gazawar gwamnatin wajen mutunta yarjejeniyarsu.
Domin Kari